SI Scholarship for Pioneering Women in STEM tana taimakawa mata daga kasashe masu tasowa irin Najeriya domin suyi karatun digiri na biyu (Master’s) a Sweden. Wannan tallafin karatun an tsara shine domin ƙarfafawa mata a fannonin kimiyya, fasaha, injiniyanci da lissafi (STEM).
Yar uwa ki sani zasu biya miki komi da komi, harda kuɗin makaranta, zasu baki Kuɗin da zaki dinga rayuwa (living expenses), da kuma kuɗin tafiye-tafiye. Ina son naga mata musamman na Arewacin Najeriya suna karatu, shiyasa na samo muku wannan babbar damar domin ku cigaba da samun ilimi mai zurfi da kuma samun nasarar ƙwarewa a fannonin da kuke. Yar uwa ku sani zaiyi kyau a matsayin ku na mata kuyi applying wannan scholarship ɗin, musamman waɗanda suke son inganta rayuwarsu. Ita dama sau ɗaya take zuwa.
Benefits | Abubuwan da zasu dauke muku.
Full tuition coverage: Yar uwa ki sani zasu biya miki kuɗin makaranta kai tsaye daga SI zuwa jami’ar ku ta Sweden a farkon kowanne semester.
Monthly stipend: Yar uwa ki sani zasu ba ki stipend na SEK 12,000 (Kuɗin ƙasar) a kowanne wata don hidimar rayuwar ki (living costs) yayin karatun. A naira sama da 1mil
Travel grant: Yar uwa ki sani zasu baki SEK 15,000 domin tafiye—tafiye (grant ɗin nan yana zuwa sau ɗaya, saidai badda wanda suke Sweden). A naira Kuɗin ya wuce 1.5mil shi sau ɗaya zasu baki wannan a shekara.
Membership in the SI Network for Future Global Professionals (NFGP): Yar uwa ki sani zaki samu damar faɗaɗa ƙwarewar sana’ar ki da haɗa kai da sauran professionals yayin da kuke karatu a Sweden.
Post-scholarship membership in the SI Alumni Network: Yar uwa, Bayan kin kammala karatunki, zaku kasance memba na wannan alumni network ɗin, wanda zai ba ku damar cigaba da samun haɗin gwiwa da ƙarin damammaki na cigaba a rayuwar ki.
Wannan tallafin babban dama ce ga Yan uwanmu mata da suyi amfani da ita don cigaba da ilimi da ƙwarewa a fannin STEM. Iyaye ku bar yayan ku mata suna karatu. Wannan sako ku turawa Yan uwanku mata domin su cike.
Ga link: https://techgono.com/si-scholarship-for-pioneering-women-in-stem/
©Abu Sultan 08069654613