Youth Action for SDG 6 Fellowship Cikakken Tallafi ne na Hadin Kai wanda za’ai a Turai wannan SDG 6 Fellowship ɗin shiri ne da aka ɗauke maka nauyin komi, ba abinda zaka kashe—su zasu ma komi, ƙungiyar International Water Association (IWA) da Grundfos suka shirya a Turai. An amince da wannan shiri a matsayin ɗaya daga cikin muhimman shirye-shirye na matasa a fannin ruwa, inda zai bada damar matasa su taka rawar gani a fannin yayi da duniya da take canzawa cikin sauri, fellowship na 2025-2026 zai mayar da hankali kan buƙatu da ƙalubalen da ke tasowa a wannan fannin.
Shekarun da ake bukata: daga 18 zuwa 35
Wuraren da za’ai wannan program ɗin da Watanni:
London, United Kingdom (Afrilu 2025)
Grundfos HQ, Denmark (Afrilu 2025)
Glasgow, Scotland (Satumba 2026)
Tallafi da zasu bayar:
Za a dauke maka nauyin waɗannan abubuwan:
- Tikitin jirgin sama (zuwa da dawowa)
- Abinci kullum (karyawa, abincin rana, da abincin dare) Kunsan ina son abinci 😀, dole na cike wannan program ɗin.🙄
- Gida kai kaɗai (saboda privacy)
- Transport daga filin jirgi zuwa otel ɗin da zaka sauka da wuraren taro
- Inshorar tafiya
- Visa su zasu ma. Babu abinda zaka kashe.
Ranar da za’a rufe wa’adin nema: 14 ga Nuwamba, 2024.
Source: Daga International Water Association da Grundfos.
Link: https://scholarshipscorner.website/sdg-6-fellowship/
Allah Bada sa’a.