Program Fellowship A Yankin Turawa. Komai Kyauta ne. Ba’a buƙatar ko sisin ka. 😊

Youth Action for SDG 6 Fellowship Cikakken Tallafi ne na Hadin Kai wanda za’ai a Turai wannan SDG 6 Fellowship ɗin shiri ne da aka ɗauke maka nauyin komi, ba abinda zaka kashe—su zasu ma komi, ƙungiyar International Water Association (IWA) da Grundfos suka shirya a Turai. An amince da wannan shiri a matsayin ɗaya daga cikin muhimman shirye-shirye na matasa a fannin ruwa, inda zai bada damar matasa su taka rawar gani a fannin yayi da duniya da take canzawa cikin sauri, fellowship na 2025-2026 zai mayar da hankali kan buƙatu da ƙalubalen da ke tasowa a wannan fannin.

Shekarun da ake bukata: daga 18 zuwa 35

Wuraren da za’ai wannan program ɗin da Watanni:

London, United Kingdom (Afrilu 2025)
Grundfos HQ, Denmark (Afrilu 2025)
Glasgow, Scotland (Satumba 2026)

Tallafi da zasu bayar:

Za a dauke maka nauyin waɗannan abubuwan:

  1. Tikitin jirgin sama (zuwa da dawowa)
  2. Abinci kullum (karyawa, abincin rana, da abincin dare) Kunsan ina son abinci 😀, dole na cike wannan program ɗin.🙄
  3. Gida kai kaɗai (saboda privacy)
  4. Transport daga filin jirgi zuwa otel ɗin da zaka sauka da wuraren taro
  5. Inshorar tafiya
  6. Visa su zasu ma. Babu abinda zaka kashe.

Ranar da za’a rufe wa’adin nema: 14 ga Nuwamba, 2024.
Source: Daga International Water Association da Grundfos.

Link: https://scholarshipscorner.website/sdg-6-fellowship/

Allah Bada sa’a.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top