SCHOLARSHIP KYAUTA NA ƘASAR TURKIYYA YARA DA MANYA ZASU IYA CIKEWA.

Wannan scholarship ɗin suna bayar da tallafin karatu ne ta hanyar daukan nauyin karatun mutum kacokam tare da ciyar da shi, ba shi muhalli da kuma kudin kashewa na iya zangunnan karatun sa.

Bangarori biyu ne. Akwai Diyanet sannan akwai IDB joint scholarships. Portal din kowannen su daban yake.

Diyanet bangaren ilimin addini ne, amma suna haɗawa da sauran ulum. Idan kuma yaro ya gama yana iya shiga wasu bangarorin. An fi samun nasu a kan ɗayan. Indai ka iya karatun Kur’ani ko ka haddace to kana da hope sosai.

IDB kuma komai da komai ne, sai abinda ka zaba. Suma suna dauka, saidai an fi competition a nan.

Tallafin ya haɗa da.
1- Wanda ya gama Junior secondary school zai tafi senior (Diyanet kawai).
2- Wanda ya kamala Senior zai tafi jami’a.
3- Wanda ya gama digiri zai je masters.
4- Wanda yake da masters zai yi PhD.
5- Wanda yake yin research.
Dukkannin wadannan ana cike su ne a portal guda.

KAFIN KA SHIGA CIKIN PORTAL DIN SAI KA FARA YIN RIJISTA. Daga nan kuma sai mutum ya shiga ya cike guraben bayanai. Ana uploading din credentials da sauran documents da za su bukata.

A LURA: Ko wane mataki akwai shekarun da idan ka wuce su to ba za ka samu shiga ba.

1- Wanda ya gama Junior secondary school zai tafi senior: kada takardar ranar da aka haife shi ta wuce shekara 15. (Wannan Diyanet kawai ya shafa)

2- Wanda ya kamala Senior zai tafi jami’a: (shekara 21)

3- Wanda ya gama digiri zai je masters: (kasa da Shekara 30)

4- Wanda yake da masters zai yi PhD: (Kasa da shekara 35)

5- Wanda yake yin research: (Shekara 45)

MAKIN DA AKE NEMA:
Suna bukatar % din SSCE/NECO/NBAIS ko TRANSCRIPT na jami’a, kamar haka:

1- Wanda ya gama Junior secondary school zai tafi senior 70% (Diyanet).
2- Wanda ya kamala Senior zai tafi jami’a. 75%
3- Wanda ya gama digiri zai je masters. 75%
4- Wanda yake da masters zai yi PhD. 75%
5- Wanda zai yi karatun da ya shafi lafiya (Medical Schools Program) 90%

ABUBUWAN DA SUKE LURA DA SHI

Idan misali aka samu dalibai duk sun cancanta amma sun wuce yawan guraben da ake da shi, to suna duba yawan % na marks. Daga nan sai su dubi sauran abubuwa kamar shekaru da sauran su.

AMMA mafi girman abin da ya fi muhimmanci a wajen su shine LETTER OF INTENT. Ita letter of intent tana daga abin da ake cike wa a portal din. Idan ka iya rubuta letter of intent mai kyau to kana da chance mai yawa akan wanda bai iya rubutawa ba. (Muna rubutawa a biya mu).

Kowa zai iya cike wa kan sa ya yi uploading, amma a bisa shawara gara idan ba ka iya ba ka nemi wadanda suka taba yi domin su yi maka. Akwai technicalities da ba lallai ne wanda bai taba yi ba ya yi su cikin sauki.

Daga karshe, idan mutum ya dace application din sa ya karbu, za su turo masa da gaiyata zuwa Abuja domin yin interview. Daga nan kuma za su tuntubi wadanda su ka dauka.

Ka da wani ya kashe maka guiwa, ko ba ka san kowa ba za ka iya ci. Mun yi wa yara da dama kuma wasu sun samu a halin yanzu ma suna can Turkiyya din suna karatun su.

Za a bude portal din daga 10/01/2025 zuwa 20/02/2025.

Ga links nan👇🏻
https://tbbs.turkiyeburslari.gov.tr/

https://dbys.tdv.org/SignIn

Do you want work with us? DM

©Abu Sultan 08069654613

1 thought on “SCHOLARSHIP KYAUTA NA ƘASAR TURKIYYA YARA DA MANYA ZASU IYA CIKEWA.”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top